A wani yunkuri na bunkasa harkokin wasanni, Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya raba cekin kudi na Naira miliyan 96 ga kungiyoyin kwallon kafa 47 na jihar da ke shiga gasar wasan kwallon kafa ta kasa. A cewarsa, kudaden za su taimaka wa kungiyoyin masu son shiga gasar ta kasa ta 2021/2022.
A cewar gwamnan, wannan tallafi zai taimaka ma gogaggun kungiyoyin kwallon wajen shiga wasannin gasar ta kasa ta shekarun 2021/2022.
Gwamnan wanda mataimakinsa Dr.Nasiru Yusuf Gawuna ya wakilta a wajen gagarumin bikin da aka gudanar a ranar Talata a dakin taro na Coronation dake gidan gwamnatin Kano.
Ya kuma bayyana cewa dukkanin kungiyoyi 10 da za su fafata a rukunin 1, kowacce kungiya za ta samu Naira miliyan 3. Kungiyoyi 29 daga rukuni na biyu, kowanne zai samu Naira miliyan 2, yayin da kungiyoyi 8 daga bangare 3, kowanne zai samu Naira miliyan 1, bi- da- bi.
“Wannan alkawari ne da gwamnatin jihar ta yi kuma ta cika” inji shi Ya kara da cewa, “Muna godiya ga masu kulab din kan kokarin da suke yi na tafiyar da kungiyoyin da kuma yadda suke jan hankalin matasa domin hakan zai hana su aikata munanan dabi’u”.
“Mun kuma yaba da kokarin hukumar kwallon kafa ta Jiha, a kan fara gudanar da gasar wasannin motsa jiki na matasa.”
Yayin da yake kaddamar da sabon mashawarcin na kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Salisu Yusuf (D–Black), Gwamnan ya umarce shi da ya kawo kwarewarsa domin ci gaban kungiyar.
“Salisu D-Black ya kware sosai, kasancewar ya horar da ‘yan wasan Super Eagles na kasa, muna da kwarin guiwa akansa ga jagorancin al’amura.
Zai mayar da kulob din zuwa matsayin da ya dace a gasar cin kofin Nahiyar Afrika. inji gwamnan.
Sai dai gwamnan ya ba da tabbacin ci gaba da bayar da goyon baya da jajircewar gwamnatin jihar wajen ci gaban wasanni.
Da yake jawabi kwamishinan matasa da wasanni Kabiru Ado Lakwaya ya bayyana shirin a matsayin ci gaban bil’adama da gwamnatin Ganduje ta bullo da shi domin bunkasa harkokin wasanni.
Daga nan sai ya bayyana cewa ma’aikatar sa na hada kai da kamfanin Coca-Cola domin horar da matasa dubu ashirin daga jihar a wani bangare na karfafa musu gwiwa.
Sauran wadanda suka yi jawabi a lokacin bikin sun hada da Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Kano, Sharu Rabi’u Ahlan, da Shugaban Kungiyar Kwallon Kafa ta Clever Warriors Dr.Najib Kurawa.