
Read Time:36 Second
Gwamnati jihar Kaduna ta kori malamai 233 bisa samunsu da takardun karatun bogi. Gwamnatin Kaduna ta ce ta sallami malamai 233, sannan zata mika su ga ma’aikatar shari’a domin a gurfanar da su a gaban kuliya, bisa tuhumarsu da laifin amfani da takardu bogi. A ranar Alhamis din da ta gabata ne hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Kaduna, (KADSUBEB), ta bayyana ta kori malamai 233 dake makarantun gwamnati a jihar, wadanda suka gabatar da shedar kammala karatun bogi domin daukar su aiki. Haka kuma, malaman da abin ya shafa za a gurfanar da su gaban kuliya, in ji hukumar ilimin.
Shugaban hukumar Tijjani Abdullahi ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Kaduna.