Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya yi kira ga Hukumar Samar da Wutar Lantarki ta Kasa (HYPADEC) da ta samar da rigunan kariya ingatattu tare da wayar da kan jama’ar da ke zaune a zagayen wuraren da ake gina madatsun ruwa domin tabbatar da tsaro a harkar samar da ruwa.
Akalla mutane bakwai ne suka rasa rayukansu,daga cikinsu akwai wani mutum da matansa biyu da babban dansa, a wani hatsarin jirgin ruwa a kauyen Zhigiri da ke karamar hukumar Shiroro ranar Lahadin da ta gabata.
Gwamna Bello, a cikin wata sanarwa da babbar sakatariyar yada labaran sa Misis Mary Noel-Berje, ta fitar a jiya Laraba, ta ce, gwamnan ya yi bakin cikin afkuwar hatsarin da ya kusan halaka iyali baki daya. Inda ta bayyana lamarin a matsayin abu mai raɗaɗi da ban tausayi.
Sai dai ya ce gina madatsar ruwa ta Zungeru ta tilastawa al’ummomin mazauna yankin da abin ya shafa su rungumi safara ta ruwa.
Gwamnan ya ce Dam din na Zungeru an yi shi ne don bunkasa samar da wutar lantarki, inda ya ce dole ne a kiyaye mutanen da ke zaune a yankunan da ke kusa da Dam din.
“Na yi bakin ciki kwarai da wannan hatsarin jirgin ruwa mara dadi; akwai bukatar a samar da matakan da za a kauce wa maimaitawar haka. Yana da kyau a sami madatsar ruwa kuma yana da mahimmanci kare mutanen da ke zaune a kusa da Dam din.”
“Addu’ata tana tare da ‘yan uwan wadanda abin ya shafa; Ina kira gare su da su dauki lamarin a matsayin wani abu daga Allah”in ji gwamnan.
Read Time:1 Minute, 22 Second
Average Rating
5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%