
Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, zai fito fili a ranar Talata mai zuwa ya bayyana sunayen wadanda suka haddasa tabarbarewar rashin tsaro a jihar.
Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Imo, Hon. Declan Emelumba ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi, a wata sanarwa da ya fitar a Owerri, babban birnin jihar Imo.
Emelumba ya ce, gwamnan zai yi amfani da taron masu ruwa da tsaki na jihar Imo karo na 6 wajen bayyana sunayen wadanda suke daukar nauyin rashin tsaro a jihar.
Emelumba ya ce, baya ga jama’a da ake ba su sunayen, gwamna zai yi wa mutanen jihar Imo bayanin irin ayyukan da ya yi a cikin shekaru biyu da ya yi a ofis.
Ya bayyana cewa, a yanzu za a gudanar da taron masu ruwa da tsaki da cin abincin rana a gidan gwamnati da karfe 12 na ranar Talata, 4 ga Janairu wannan shekara ta 2022.