
Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya kori kwamishinan lafiya na jihar, Farfesa Princewill Chike, saboda gudanar taro karbar bakuncin taron share fage na kungiyar likitoci da hakora ta Najeriya, MDCN, a Fatakwal bada izinin gwamnatin jihar b karbar bakuncin taron share fage na kungiyar likitoci da hakora ta Najeriya, MDCN, a Fatakwal.
Gwamnan ya bayyana matakin da Kwamishinan ya dauka na karbar bakuncin taron kungiyar ba tare da amincewar gwamnatin jihar Ribas ba a matsayi abin kunya.
Wata sanarwa da mataimaki na musamman ga gwamna Nyesom Wike kan harkokin yada labarai, Kevin Ebiri, ya fitar a ranar Litinin, ta ce gwamnan ya sanar da korar Farfesa Chike ne a lokacin da shugaban kungiyar likitoci da hakori ta Najeriya Farfesa Abba Wasiri Hassan ya kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa dake gidan gwamnati a Fatakwal jiya Litinin.
Gwamnan ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Ribas ba ta taba neman karbar bakuncin taron share fage na Majalisar Likitoci da Hakora ta Najeriya a Fatakwal ba, yana mai jaddada cewa Kwamishinan Lafiya ya yi kuskure wajen shirya taron kungiyar, a lokaci da Gwamnatin Jihar ta dakatar da kaddamar da ayyuka.
“A gaskiya ban taɓa ganin abin kunya irin wannan ba a rayuwata.
Gwamnan ya ce,“Kowa ya san cewa ba dabi’a ta ba ce in gayyato mutane, kuma ba za ku iya karbar bakuncinsu ba. Don haka duk wanda ya yi haka zai jawo ma kansa.”
Wike ya ce bukatar da kungiyar MDCN ta yi na cewa gwamnonin jihohi su samar da manyan asibitoci guda daya a kowace mazabar dan majalisar dattawa, ba za ta tabbata ba saboda karancin kudade.
“Kun yi magana a kan samun babban asibiti a kowace mazabar dan majalisar dattawa, kun san ba zai yiwu ba”.
Gwamnan ya bayyana cewa a wani yunkuri na inganta rayuwar ‘yan kasa wajen samar da ingantaccen kiwon lafiya, gwamnatinsa ta fara aikin gina wasu asibitocin shiyya a Bori, Degema, Etche, Ahoada da Omoku.
Ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta kuma kashe makudan kudade wajen bunkasa ilimin likitanci a jihar, musamman tare da kafa Kwalejin Kimiyyar Kiwon Lafiya ta Jami’ar Jihar Ribas tare da bayar da tallafin kudin karatu a duk shekara ga ‘yan asalin jihar 130 da ke karatun likitanci a PAMO University of Medical Sciences.
Shugaban MDCN, Farfesa Abba Wasiri Hassan, ya yaba wa Gwamna Wike bisa kyakkyawar dabi’arsa ga harkokin kiwon lafiya, da bayar da magunguna a jihar Ribas, musamman yadda aka zuba jari a Kwalejin Kimiyyar Kiwon Lafiya ta Jami’ar Jihar Ribas, da bayar da guraben karatu ga ‘yan asalin jihar da ke karatun aikin likita.