
Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya bukaci ‘yan Najeriya da su tsammaci zuwan kyawawan abubuwa da za su zo masu a wannan shekara ta 2022, yana mai cewa, sabuwar shekarar tana dauke da abubuwa masu kyau da basu da iyaka.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labaran sa, Abdu Labaran Masari.
Da yake bayyana fatan alheri ga ‘yan Najeriya, a wannan sabuwar shekara ta 2022, gwamna Masari na jihar Katsina ya ce, idan aka yi la’akari da cewa shekarar 2022 za ta zama shekarar karshe ta mulkin Shugaba Buhari da wasu gwamnonin jihohi, za a samu karin amfani a kokarin gwamnatocin Kasa da jihohi na sanya rage damuwa ga ‘yan kasar.
Ya ba da tabbacin cewa, yaki da rashin tsaro zai tabbatar da ingantaccen tsari wanda ba zai bar wa masu laifi damar yin numfashi ba.
Gwamnan, ya koka da kalubalen da cutar Covid 19 da ‘yan fashi ke haifarwa, ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta janye duk wata hanya, da sanya hannu a kan kawo karshen ayyukan ta’addanci a jihar, Sai dai ya yi kira da a kara ba da hadin kai ga gwamnati, domin ba ta damar samun karin nasarori a sabuwar shekara.