
Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya bayyana ra’ayinsa kan abin da ya kamata a yi domin fatattakar ‘yan bindiga da ke addabar al’ummar jihar.
El-Rufai ya ce, ya kamata jami’an tsaro su tada dazukan ta hanyar rowan bama-bamai a inda ‘yan bindigar suke.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake magana a gidan Talabijin na Arise a jiya Litinin. Gwamnan ya ce, ana iya dasa itatuwa a wuraren da ke kusa da dajin da abin ya shafa daga baya.
Sai dai ya yarda cewa tayar da kafet a dazuzzukan zai haifar da barna.
El-Rufai ya lura cewa, irin wannan matakin zai bunkasa Noma a yankunan karkara.
Gwamnan ya ce rashin isassun ma’aikata ne ya jawo gazawar iyawar jami’an tsaro na tsawon lokaci wajen dakile ‘yan fashi a yankin Arewa maso Yamma.
A cewar gwamna El-Rufai;“Wadannan ‘yan ta’addan suna gudanar da ayyukansu ne a yankin domin maboyarsu tana cikin dajin.Wannan babbar matsala ce. Jami’an tsaro suna yin iya kokarinsu, amma ‘yan taddan sun fi karfinsu.”
“Gaskiyar magana ita ce, ba mu da isassun kayan aiki a kasa don fuskanta da magance dimbin kalubalen tsaro, kuma wadannan kalubalen tsaron, sun yadu, kuma babu wani bangare na Najeriya ko daya da ba shi da matsalar tsaro.
“Na yi imani a koyaushe cewa,ya kamata mu tada bam a cikin dazuzzuka; za mu iya sake dasa bishiyoyi bayan Mun jefa bama-bamai a cikin dazuzzuka, mu jefa bama-bamai duka.” Ya jaddada