
Read Time:36 Second
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya yi alhinin rasuwar Olubadan na Ibadan, Oba Saliu Adetunji wanda aka sanar da rasuwarsa ranar Lahadi yana da shekaru 93 a duniya.
Gwamnan a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa, Muhammed Onogwu ya rabawa manema labarai yayin da yake mayar da martani game da rasuwar mahaifinsa, ya bayyana rasuwarsa a matsayin rashi na kasa ganin cewa Najeriya ta yi rashin wani babban uban gargajiya.
Gwamna Bello ya yi nuni da cewa, duk da cewa mutuwar tasa ta zo a lokacin da ya tsufa sosai, amma aikin da yake yi na neman zaman lafiya da hadin kai zai kasance cikin kewar sa a jihar da yankin da ma kasa baki daya.