
Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya bayyana matukar alhininsa game da kisan gillar da aka yiwa kwamishinan kimiya da fasaha
Dr. Nasir, wanda aka tsinci gawarsa a bandakin gidansa da ke rukunin gidajen Fatima Shema a ranar Alhamis da ta gabata.
Da yake bayyana kisan a matsayin rashin tausayi, Gwamna Masari wanda a bayyane abin ya girgiza shi ya ce, abin takaici ne yadda aka yanke wata rayuwa mai cike da alƙawari, ta hanyar amfani da wuƙa, da masu kisan gilla suka yi. Yana mai shan alwashin cewa gwamnati za ta yi abin da ya kamata don kamawa tare da hukunta wadanda suka aikata wannan aika-aika.
Ya ce abin takaici ne yadda za a yanke ma irin wannan matashin rayuwa ba zato, ba tsammani. Ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai himma da kwazo, da aminci wanda bai taba kasawa a duk wani aiki da aka ba shi ba.
A cewar Gwamnan, rasuwar Kwamishinan babban rashi ne ga jihar Katsina.
Da yake jajantawa iyalan marigayin da suka hada da mata da ‘ya’ya da mahaifiya tsohuwa da ’yan’uwa da dama. Gwamnan Jihar Katsina ya bukaci iyalan mamacin da yin hakuri, tare da jajanta musu bisa ganin cewa babu makawa mutuwa tana kan kowane mai rai.
Dr. Nasir ya yi rayuwa mai cike da abin koyi duk da karancin shekarunsa a
Duniya.