
‘Yan kasuwa da dama a shahararriyar kasuwar Balogun da ke jihar Legas sun yi kuka a safiyar ranar Alhamis yayin da gobara ta kona kayansu.
Gobarar da ta tashi da tsakar dare ta faru ne kwanaki tara kafin Kirsimeti.
Da yawa daga cikin ‘yan kasuwar sun koka kan yadda suka tanadi miliyoyin kayayyaki domin sayar da su a karshen shekara kafin tashin gobarar.
Abc news ta tattaro cewa yawancin ‘yan kasuwa da ke sayar da tufafi da jakunkuna ne suka fi samun matsala.
Daya daga cikin ‘yan kasuwar da abin ya shafa, mai suna Iya Akande, ta fashe da kuka a lokacin da yake bada labarin lamarin.
Ta koka da yadda wasun su ke karbar lamuni don siyan kaya gabanin Kirsimeti da sabuwar shekara.
“Na zo kasuwa ne don bude shagona, sai na ga ‘yan kasuwa da yawa suna kuka. Na daga kai na ga an kone kayanmu da wuta.
“Muna cikin matsala. Da yawa daga cikinmu sun karbi lamuni don samun kayayyaki domin mu samu riba mai yawa a lokacin bukukuwan.”
Da aka tambaye ta kimanta adadin kayan da suka kone, ta ce, “miliyoyin”.