
Janar Manajar hukumar kiyaye muhalli ta Jihar Kaduna Maimunatu Abubakar, ta bayyana cewa jami’an hukumar za su fara gudanar da aikin duba muhalli a duk fadin Jihar Kaduna a cikin watan Janairu 2022 domin tabbatar da al’amuran lafiya da na muhalli sun ci gaba da inganta.
Maimunatu Abubakar ta bayyana hakan ne lokacin da take ganawa da manema labarai a ofishinsa da ke hukumar KEPA cikin garin Kadina.
Maimunatu Abubakar ta ci gaba da cewa tuni shirye shirye sun yi nisa wajen ganin jami’an sun shiga Gida Gida,kwararo kwararo wato layi layi domin tabbatar da tsafatar muhalli.
“Zamu shiga ko’ina da ina saboda haka kamar yadda doka ta ba mu ikon gudanar da aiki idan muka ga mutane sun kasa gyara kwatar da suke amfani da ita ko wata kazantar da bai kamata a gani a inda mutane ke zama ba hakika zamu hukunta mutum ko waye, domin muna da kotun tafi da gidanka wadda za ta zartarwa da mutum hukunci kamar