
Samuel Eto’o, ya lashe zaben shugabancin hukumar kwallon kafa ta Kamaru (FECAFOOT).
Kuma fitattun taurarin Cote d’Ivoire, Didier Drogba da Yaya Toure ba da ɓata lokaci suka aikewa ma Eto’o sakon taya murna, bayan nasarar dare kujerar shugabancin kungiyar kwallon kafa ta kasar Kamarun da ya samu a ranar Asabar, 11 ga Disamba, 2021.
Tsohon dan wasan Barcelona da Real Madrid, ya lashe zaben da kuri’u 43, yayin da ya doke abokin takararsa, kuma shugaban rikon kwarya, sannan mataimakin shugaban hukumar CAF, Seidou Mbombo Njoya wanda ya sami kuri’u 31.
Nasarar da dan wasan mai shekaru 40 ya samu, ta biyo bayan buga wasa mai kayatarwa da ya yi, a lokacin da yake taka leda, wanda ya sanya shi ya sami nasarar lashe manyan kofuna a duniya, ciki har da gasar cin kofin Nahiyar Afirka, da gasar cin kofin zakarun Turai, da FIFA Club, World Cup, da La Liga, inda ya kuma sami kyaututtuka da dama.
A sakonnin fatan alheri da suka aika masa, abokan hamayyarsa a filin wasa kuma abokansa a bayan fage, Drogba da Toure, sun bayyana nasarar da abokin nasu ya samu a ranar Asabar, a matsayin wani mataki na farfado da kwallon kafa a Nahiyar Afirka.
Drogba ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa “Ina taya Samuel Eto’o murnar wannan zabe na shugaban hukumar kwallon kafar Kamaru.”
“Barka dai Shugaba! Abin ban mamaki ganin abokina Samuel Eto’o yana samun daukaka, kuma an zabe shi a matsayin shugaban hukumar kwallon kafa ta Kamaru (FECAFOOT)
Shi ma .” Tuore ya wallafa a shafin sa na Twitter cewa, “Shugaban! Labari mai ban mamaki .”
Eto’o, a cikin sakon godiyarsa ga masu zabe da magoya bayansa, ya bayyana nasarar da ya samu a matsayin abin alfahari a rayuwarsa.
.