
Shugaban kasar Botswana Mokgweetsi Masisi, ya kamu da cutar Korona virus,an kuma tilasta masa killace kansa.
Mai magana da yawun gwamnatin kasar ya bayyana haka a jiya Litinin.
“alamun cutar ya bayyana ga Shugaban, kuma yana karkashin kulawar likita.”
Mataimakin shugaban kasar Slumber Tsogwane ne zai maye gurbinsa har sai abinda hali ya yi.
An fara gano wannan cuta ta korona nau’in Omicron,a Botswana da Afirka ta Kudu a ƙarshen watan Nuwamban shekarar da ta gabata. Kwanannan ne,kasar Botswana ta sanar da kaddamar da wani gangamin karfafa wa wadanda aka riga aka yi musu allurar rigakafi,tare da rage shekarun yin allurar ga yara zuwa shekaru 12.
Omicron na haifar da wani sabon bala’in annoba a duniya, inda a halin yanzu ta yadu cikin kasashe kusan 100, a cewar hukumar lafiya ta duniya(WHO).
Cutar tana da saurin yaduwa, tana shafar mutanen da aka yi wa allurar rigakafi da kuma wadanda suka taba kamuwa da cutar. Yayin da kasashe da yawa ake ba da sanarwar tsauraran matakan kiwon lafiya, tare da adadin sabbin cututtukan da ke faruwa a kullun.