–
Canja jamiyya ba za ya sauya rashin sa’ar PDP ba. -jam’iyyar APC
Jamiyyar APC reshen jihar Legas, ta ce, sauya shekar wata kungiyar da ta balle daga jamiyyar APC zuwa jamiyyar PDP, ba za ya iya sauya rashin nasarar babbar jamiyyar adawar a jihar ba.
Sakataren Yada Labarai na Jamiyyar APC a Jihar Legas, Mista Seye Oladejo, ne ya bayyana hakan a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a ranar Lahadin da ta gabata a Legas, lokacin da yake mayar da martani kan sauya sheka da wasu yayan jam’iyyar APC , da suka fusata suka koma PDP ranar Asabar.
Ba wani abu da zai faru da zai canza rashin nasarar PDP. Kullum suna rashin nasara ne, rashin nasara yana cikin jininsu ne. Don haka, za su sake yin rashin nasara”.
Don , sun koma , ba komai, za mu hadu a rumfunan zabe. Ina mai tabbatar muku da cewa ba za su samu ko da shiyya daya ba a jiharmu”.
inji shi.
A cewarsa, yunkurin wasu yan jamiyyar da suka fusata, ya nuna butulcinsu na siyasa domin sun yi tunanin za su iya kawo wani ariziki na musamman da ba a san shi ba, bare kuma a jiharmu.
Oladejo ya ce yanzu haka kungiyar da ake ce ma Legas 4 Lagos ta kafa jamiyyar adawa, kuma jamiyya mai mulki ba za ta yi asarar kungiyar ba.
Dangane da batun sasantawa da kungiyar, Oladejo ya ce babu wanda ya kori wadanda suka yi rauni daga jamiyyar.
Idan suna so su dawo a yi tafiyar da su, Jamiyyar siyasa ce, ba ma rufe kofa ga kowa”.
Da fatan wata rana za su ga haske. Su sani cewa Legas ta kasance jiha ce mai ci gaba, kuma ta kasance daya. Suna iya dawowa.”
“idan suna son dawowa nan gaba me zai hana? Ƙofofinmu a buɗe suke har abada ga waɗanda suke shirye su tuba su ga haske,” in ji shi.
Dangane da kokarin da APC ke yi na sulhunta wasu kungiyoyin da ke cikin jamiyyar kamar (Conscience Forum), kungiyar (AAMCO) da kuma jamiyyar (Democrat) Oladejo ya ce tsarin sulhu a jamiyyar a bude yake.