
A jiya Talata ne gwamnatin Burtaniya ta cire Najeriya da wasu kasashen Afirka 10 daga cikin jerin kasashen da ta haramta zirga-zirgar jiragen sama daga kasashen Afirka biyo bayan bullar cutar Curona wadda ake ma lakabi da Omicron a Afirka ta Kudu.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta bai wa kamfanin Air Peace gurbi guda bakwai domin kawo karshen takaddamar diflomasiyya da Najeriya.
A cewar wata sanarwa da babbar hukumar Biritaniya ta fitar jiya a Abuja, wannan matakin ya biyo bayan nazari na baya-bayan nan da hukumar kula da lafiya ta Burtaniya ta yi, inda ta jaddada cewa za a cire Najeriya da sauran kasashe 10 da ke cikin jerin sunayen. daga karfe 4 na safiyar yau Laraba 15 ga Disamba.
A baya jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa, makwanni biyu kacal bayan gabatar da wannan jerin kasashe, za a soke wannan jerin sunayen, biyo bayan matsananciyar matsin lamba daga matafiya na Najeriya da gwamnatin Najeriya, lamarin da ke barazanar daukar fansa.
Gwamnatin Burtaniya ta kara da Najeriya cikin jerin wadanda ta hana tafiye-tafiye daga ranar Litinin 6 ga watan Disamba, inda ta bayyana cewa mutanen da ke tafiya Burtaniya daga kowace kasa za su bukaci yin gwaji daga watan Disamba.