
Babbar jam’iyyar adawa a Burkina Faso, CDP, ta sake da zaben Eddie Komboïgo a matsayin shugabanta.
An gudanar da zaben ne a jiya Lahadi a lokacin babban taro karo na 8 a Ouagadougou babban birnin kasar.
Jam’iyyar ta gabatar da wani sabon kwamitin siyasa mai kunshe da mambobi 89 abinda ke nuna wani sauyi ga jam’iyyar da aka kafa shekaru 25 da suka gabata.
“Na gode maku kuma ina tabbatar maku cewa kun yi zabi mai kyau. Na yi alkawarin gudanar da adalci a jam’iyyar. Zan yi aiki tukuru don fuskantar babban yakin neman zabe.”in ji sabon shugaban jam’iyyar Congress for Democracy and Progress Party.
Jam’iyyar ta tabbatar da tsohon shugabanta Blaise Campaoré a matsayin shugaban kasa mai daraja kuma ta sha alwashin kara tabbatar da hadin kan cikin gida.
“Mun yanke shawarar ci gaba da rike shugaba Blaise Compaoré a matsayin shugaban kasa mai daraja,kuma mun janye dukkan tuhuma da aka yi masa,” in ji zababben shugaban.
Eddie Komboïgo ya yi alkawarin aiwatar da wani gagarumin shirin garambawul da nufin kara tallafi a tsakanin talakawa.