
Read Time:37 Second
Babban mai shigar da kara na majalisar dattawan Najeriya, Sanata Orji Uzor Kalu, ya ce bai karya wata doka ba ta hanyar ziyartar shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu da ake tsare da shi.
Kalu, tsohon gwamnan jihar Abia yana maida martani ne kan ikirarin Barr. Ifeanyi Ejiofor, lauyan Nnamdi Kanu cewa ya keta doka ta hanyar ziyartar shugaban kungiyar IPOB dake tsare a hannun hukumar tsaron kasar (DSS).
A cewarsa, Ejiofor ya fusata ne domin ba ya kusa ta yadda zai sauraron hirarsa da Kanu a lokacin ziyarar.
Ejiofor a wata sanarwa da ya fitar ya ce, Sanatan ya saba umarnin kotu, inda ya ziyarci wanda yake karewa dake tsare a hannun hukumar tsaro ta DSS a Abuja.