
Ministan yada labarai da al’adu Alhaji Lai Mohammed ya ce, ba don ayyukan shugaban kasa Muhammadu Buhari ba, da ‘yan ta’adda sun shelanta daular Musulunci a Najeriya.
Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja yau Laraba, Ministan ya ce,al’ummar da za tu zo nan gaba, za ta yi wa Buhari addu’ar alheri, wanda ya ce ya sanya tsaro ya zama babban abin da gwamnatinsa ta mayar da hankali a kai.
Tun hawansa karagar mulki a shekarar 2015, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ci gaba da mayar da batun tsaro a matsayin babban aikin da ya sa gaba.
Wannan ba wani abin mamaki ba ne, duba da yadda yaki da rashin tsaro na daya daga cikin abubuwa uku da gwamnatin ta sa a gaba.
Lai, ya kara da cewa, “Abu ne mai sauki mu manta daga inda muka fito. A yau, muna duban halin da ake ciki ne kawai, ba tare da tunanin me zai faru ba idan da a ce wannan Shugaban kasa bai tari aradu da ka ba, dangane da batun tsaro.
“Kamar yadda ‘yan tada kayar baya suka yi kafin zuwan wannan Gwamnati,da yin iko da wani fili mai fadin kasar Belgium, tare da kai hare-hare irin na masu tayar da kayar baya a kusan jihohi goma sha biyu, ciki har da babban birnin tarayya wanda aka kai hari akalla sau biyar a wasu lokuta, watakila da sun cimma burinsu na shelanta daular Musulunci a Najeriya, in da shugaba Buhari bai taka rawar da ta dace ba.
“Bayan haka, a cikin shekarar 2014, Boko Haram sun shelanta Halifanci a Gwoza bayan sun kwace Bama da Gamboru da sauran garuruwa da kauyuka a Borno, Yobe da Adamawa. Sun nada sarakunansu ne, sun karbi haraji kuma suka daga tutarsu kafin sojoji su fatattake su,” inji Lai Mohammed.