
An gano gawar wani bakon haure da ake kyautata zaton dan Najeriya ne a wani dajin da ke kusa da kan iyakar Poland da Belarus, kamar yadda ‘yan sandan kasar Poland suka bayyana a yau Laraba, mutuwar ta baya-bayan nan ta haifar da rudani a kan iyakar kasashen Turai da ke gabashin kasar.A cewar kamfanin dillancin labaran AP, an bayar da rahoton mutuwar ne kwana daya bayan da wata kungiyar agaji ta ce ta yi imanin cewa wata yarinya ‘yar kasar Iraki mai shekaru hudu ta bace a wani yanayi sanyi a yankin Poland na kan iyaka da kasar Belarus.Kungiyar Border Group, wacce ta hada da ‘yancin ‘yan gudun hijira, da sauran kungiyoyin kare hakkin bil’adama, ta ce, yarinyar ta rabu da iyayenta, inda ta yi zargin cewa jami’an tsaron kan iyakokin Poland ne suka tura iyayen suka tsallaka kan iyakar kasar zuwa Belarus.Sai dai hukumar kare kan iyaka ta Poland ta musanta hakan, tana mai cewa ba ta tsare wasu iyalai ba. ta ce bayan samun bayanan da masu fafutuka suka baiwa kwamishinan kare hakkin dan adam na kasar, hukumomi sun binciki yankin ta sama da kasa domin neman yarinyar.