
Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya ce jami’an tsaro sun fatattaki ‘yan ta’addar Boko Haram da suka kutsa kai cikin jihar.
Ya bayyana hakan ne jiya a Abuja bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ganawar daban da shi da takwaransa na jihar Taraba Darius Ishaku kan rashin tsaro.
Gwamna Sule ya shaidawa manema labarai na fadar gwamnatin jihar cewa ya gana da shugaban ne domin nuna jin dadinsa da irin goyon bayan da jiharsa ke samu kan harkokin tsaro.
Ya ce, “Na zo ne domin nuna godiya ga shugaban kasa bisa duk goyon bayan da muke samu a fannin tsaro.
“Tabbas kun ji cewa, akwai ayyukan hadin gwiwa mai karfi na runduna ta musamman; Sojoji da ‘yan sanda tare da ‘yan banga da sojojin sama da na ruwa a kananan hukumomin biyu da ke kan iyaka da Abuja kuma a sakamakon haka ayyuka daban-daban sun samu nasara sosai.
“Kwanan nan, an kai hari ga wasu makarantunmu, aka tuntube mu a asirce aka daukar matakai, sannan mun gode wa Allah da ya ba mu ikon korar wadancan ;yan ta’dda,” inji shi.
Akan mayakan Boko Haram da suka taru a sassan jihar, ya ce yanzu an tarwatsa su.