
Wata dattijiya mai fafutukar,mai suna High Cif Josephine Ezeanyaeche, ta bukaci shugabannin kasar nan da su tabbatar da cewa, Najeriya ta ci gaba da kasancewa kasa daya dunkulalla da ba za a iya raba ta ba, a daidai lokacin da ake ci gaba da kiraye-kirayen da kai kasar ta wargaje. Ezeanyaeche, mai shekaru 102 wadda aka fi sani da “Mama Africa” ta yi wannan kira ne lokacin da ta ziyarci Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Abuja ranar Talata. Ezeanyaeche, wacce kuma ita ce ta kafa kungiyar masu fafutukar kare hakkin jama’a, mai suna ‘muryar manyan ‘yan Najeriya’ ta ce, ta fara ziyarar ba da shawarwari ga gidajen yada labarai domin tabbatar da zaman lafiya da hadin kai ga Najeriya, wadda ita ce babbar kasa a Afirka. A cewar ta, ziyarar wani bangare ne na yakin neman zabe da kungiyar ta ta ke yi na wayar da kan al’umma kan matsalolin da ke addabar mata da yara. Ta kuma bayyana cewa ziyarar na da nufin karfafa kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na tabbatar da hadin kai da kuma hana tada zaune tsaye a kasar nan.
‘Yar gwagwarmayar ta ce burinta a matsayinta na ‘yan shekara dari, shi ne ta ga gwamnati ta hada kan ‘yan kasa don yin aiki tare, gami da martaba Najeriya a matsayinta na giwar Afrika, tana mai cewa ana sa ran Najeriya za ta nuna misali da jagoranci a Afirka.
Ta kara bayyana fatarta na ganin ‘yan kasar na gudanar da harkokinsu bai daya.
“Buri na shi ne ganin Najeriya ta hada kan ‘yan kasarta wajen gudanar da harkokin kasuwanci, ta yadda za ta jagoranci Afirka wajen samun hadin kai,da ci gaba a dukkan fannonin na harkokin dan Adam.”