
MInistan Kudi na kasar Zambia Situmbeko Musokotwane a ranar Talata ya bayyana cewa,akwai yiwuwar kasar ta nemi hukumar bada lamuni ta duniya ta tsawai ta mata lokacin da zata biyata bashin da take binta , bayan da wa’adin biyan ya yi.
“Nauyin bashin dake kan kasar ta Zambia shi ne tushen wasu munanan matsalolin zamantakewa da tattalin arziki da kasar ta fuskanta a cikin ‘yan shekarun da suka gabata,” in ji Musokotwane.
Bashi
Zambiya na iya neman tattaunawa da masu binta bashin domin tsawaita biyan basussukan da ta cimma, bayan cimma yarjejeniya ta farko da asusun lamuni na duniya IMF.
Zambia, na daya daga cikin manyan kasashe masu samar da tagulla a duniya, ta zama kasa ta farko a Afirka da ta yi kasa a gwiwa wajen yaki da cutar COVID-19 a watan Nuwambar 2020, bayan shekaru da dama da gwamnatin ta yi na ciyo bashin da ake binta wanda ya haura kashi 120 cikin 100 na tattalin arzikin da kasar take samarwa a shekara.
Musokotwane a wani jawabi da ya gabatar a majalisar dokokin kasar ya ce, kudaden harajin da Zambia ke samu a halin yanzu, ba su isa su biyan albashin gwamnati da basussukan ayyukan kasa.
“Faduwar darajar kudin kasar kwacha, da hauhawar farashin kayayyaki, da kuma rufe wasu kasuwanni, duk sakamakon karbo rancen da ya wuce kima ne”, in ji shi.
A na bin kasar bashin sama da dala biliyan 14 daga waje, ciki har da lamuni da aka tabbatar ga kamfanonin gwamnati.
A ranar Juma’a ne asusun bada lamauni IMF da Zambia suka cimma yarjejeniya ta matakin ma’aikata kan dala biliyan 1.4, da tsawaita ayyukan lamuni na shekaru uku, wanda ya zo ma kasar lokaci daya da na cikar wa’adin biyan bashin.