
Bayan kwashe Watanni bakwai da komawarsu kauyukansu a karkashin kariyar jami’an tsaron, da kuma lamunin shugaban jamhuriyar ta Nijer Bazoum Mohamed, al’ummar Anzourou na sake barin kauyukan nasu,sakamkon ta’asa das ace-sacen dabbobi da mayakan jihadi suke yi akan iyakar Nijer da Ancourou ta kasar Mali. inda har yanzu kungiyoyin masu dauke da makamai ke ci gaba da kai hare-hare.
A watan Agustan 2020, an kashe fararen hula da sojoji 19 a wani masallaci. A yau, ana ci gaba da fuskantar barazanar ta’addanci sannan an umurci mutanen yankin da su bar yankin.
Sama da mutane 4,000 da suka hada da mata da kananan yara yanzu haka sun tsere daga yankin saboda barazanar tsaro daga masu jihadi. Yawancin al’ummomin da ke gudun hijira a yanzu sun fake a wani yanki da ke kusa da ake kira Sarakoira.
Daya daga cikin mutanen da suka yi gudun hijira ya shaida ma majiyar mu cewa,“A yau muna cikin yunwa da kishirwa, muna rayuwa cikin wahala sosai a wannan sansani, lokacin da ‘yan ta’addan suka kai hari a masallacin kauyenmu. Sun kashe mutane bakwai daga cikin iyalina da kannena da mahaifi na da kuma kawuna ta,”
“Sun zo ne a kan babura, sun kashe iyalanmu, sun sace mana shanu, mun bayar da sanarwar, amma ba mu samu wani taimako ba, jihar ta yi watsi da mu, shi ya sa muka sake barin kauyenmu.”
A cikin shekaru uku da suka gabata, an rufe makarantu da cibiyoyin kiwon lafiya sakamakon hare-haren da masu jihadi ke kai wa.