
Kungiyar Gwamnonin Arewa Maso Yamma ta Bayar da Tallafi ga Iyalan da ‘Yan Bindiga Suka Hallaka a Sokoto
Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Yamma, ta bayar da gudummawar zunzurutun kudi har Naira Miliyan Hamsin (50) ga dangi da ‘yan bindigasuka hallaka kwanannan a kauyen Gidan Bawa da ke karamar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato.
Shugaban kungiyar, Aminu Bello Masari na jihar Katsina ne ya sanar da bayar da tallafin a lokacin da ya ziyarci fadar gwamnatin Sokoto domin jajantawa gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal da kuma gidan Sanata Aliyu magatakardar Wamako mai wakiltar Sokoto ta Kudu a majalisar dokokin kasa.
Gwamna Masari wanda ya samu rakiyar takwaransa na jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa, Gwamnonin Arewa maso Yamma tare da na Plateau, Neja da Nasarawa suna aiki kafada-da kafada da Gwamnatin Tarayya wajen samar da dabaru da hanyoyin magance matsalar rashin tsaro wanda tuni aka fara aiwatar da su.
Gwamnan na Katsina ya bayyana fatansa na ganin cewa za a shawo kan ta’addanci,hadin gwiwa da gwamnatin tarayya, tare da daukar dubarun fasahar zamani.
Masari ya kuma yi kira ga ‘yan majalisar tarayya da su tashi tsaye wajen sauke nauyin da kundin tsarin mulkin kasar ya rataya a wuyansu ta hanyar samar da wasu dokoki da za su dace don magance matsalolin rashin tsaro a kasar nan.
Haka kuma, Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya koka kan yadda shugabannin da suka gabata suka yi sakaci wajen yin amfani da dajinmu wajen daidaita yanayin da ya sa Fulani masu rinjaye suka mayar da shi a matsayin mafakar ‘yan fashi.
A cewarsa, kwato dajin a yanzu yana bukatar amfani da fasahar zamani wajen samar da sahihin bayanai na makiyaya da Dabbobi a cikin jerin gwanon motocinsu kamar yadda gwamnatin jihar Kano ta yi a dajin Falgore.
A nasa jawabin, Sanata Aliyu Wamako a lokacin da yake yaba wa kungiyar gwamnonin Arewa maso Yamma, ya ce akwai bukatar a samar da isassun jami’an tsaro domin yakar ‘yan fashi da makami.
Sanatan ya kuma jaddada cewa akwai bukatar a shirya taron bai-daya na masu ruwa da tsaki domin bayyana gaskiyar lamarin tare da bayar da shawarar matakan da suka dace domin kawo karshen matsalar rashin tsaro a kasar.