
Read Time:24 Second
Gwamna Aminu Bello Masari ya jagoranci tawagar wakilan Dattawan jihar Katsina domin ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari a kan al’amuran da suka shafi jihar, musamman tsaro da kuma Asibitin Koyarwa na Jami’ar Umar Musa Yar’adua dake Katsina.
A cikin wannan tawaga akwai Ministan Zirga-zirgar jiragen sama Sanata Hadi Sirika, Sanata Mamman Abubakar Danmusa, Sanata Abba Ali, da Alhaji Yusuf Nalado.
Haka kuma a wannan zama akwai Shugaban Ma’aikata na Fadar Shugaban kasa Ambasada Ibrahim Gambari da Ministan Lafiya Dokta Osagie Ehanire.