
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da gwamnatin Burkina Faso domin dakile da kuma hukunta masu safarar mutane.
A wata sanarwa da Kakakin hukumar hana fataucin bil-Adama ta kasa Adekoye Vincent, ya fitar jiya Lahadi, ya bayyana cewa, an rattaba hannu kan sabuwar dokar ne a babban taro na 3 na hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Burkina Faso da aka gudanar a otal din Transcorp Hilton da ke Abuja.
A tabakinsa, yarjejeniyar dakile hana fataucin biladama, ana sa ran za ta kara matsin lamba kan masu safarar mutane da kungiyoyinsu, da suke gudanar da ayyukansu a cikin kasashen biyu. Haka kuma, wannan yarjejeniyar ta zo ne bayan ‘yan makonni da aka kulla irin wannan yarjejeniya tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Nijar.
Jakadan Najeriya a Burkina Faso Mistura Abdulkareem ne ya sanya hannu a takardar a madadin Najeriya shi kuma jakadan Burkina Faso a Najeriya, Piabie N’DO ya sanya wa hannu a madadin kasarsa.
Darakta-Janar na Hukumar NAPTIP, Fatima Waziri-Azi, ta ce yarjejeniyar ta zama babban barazana ce ga ayyukan masu safarar mutane.
Darakta Janar ta hadin gwiwar kasashen biyu, Bakyonon Kanzie, ta ce kasarta za ta aiwatar da dukkan bangarorin yarjejeniyar domin a mfanin kasashen biyu