Read Time:32 Second
Hadaddiyar kungiyar kwadago a Najeriya a jiya Litanin , ta bukaci ‘ya’yanta su kasance cikin shirin dakile gwamnatin tarayya muddin ta aiwatar da shirinta na karin kudin Man fetur zuwa 340 a shekara mai kamawa.
Kungiyar ta ce, ba zata rungume hannuwa ba tana kallon gwanmatin ta kara takura ma ‘yan kasa wadanda tuni talauci ya kassara..
Kungiyar ta kara da cewa, duk wani yunkurin karin farashin mai, zai shafi kowane dan Najeriya, ba tare da la’akari da matsayinsa ba.
Gwamantin tarayyar Nijeriya a watan da ya gabata ta bayyana shirinta na yiwuwar karin farashin man fetur, duba da matsalolin tattalin arziki da gwamnagin ke fuskanta.