
Gwamnatin tarayya, ta tsawaita aikin hada layin wayoyi da lambar zama dan kasa ta NIN zuwa Talatin da daya ga watan maris na wanna shekara.
Sai dai wata sanarwar hadin gwiwa da Hukumar Sadarwa ta Najeriya NCC da Hukumar Kula da Shaida ta Kasa (NIMC) suka fitar a jiya Juma’a ta ce, adadin wadanda suka yi rajistar NIN ya karu zuwa miliyan 71.
Sanarwar mai dauke da sa hannun mai magana da yawun hukumar NCC da na NIMC, Ikechukwu Adinde da Kayode Adegoke, ta ce “karin wa’adin ya biyo bayan bukatar da masu ruwa da tsakin suka yi, da suka hada da ‘yan kishin kasa da kuma yan Najeriya mazauna kasashen waje.
Wannan tsawaita wa’adin zai baiwa gwamnatin tarayya damar karfafa nasarorin da aka samu da kuma hanzarta shigar da yan Najeriya a muhimman wurare, da suka hada da lungu da sako da makarantu da asibitoci da wuraren ibada.”