
Yayin da sabuwar shekara ke kamawa, an kashe mutum guda tare da sace akalla mutane goma sha biyu da suka hada da mata goma, a lokacin da gungun ,barayin daji suka kai farmaki a kauyen Kerawa dake karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.
Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban matasa na kauyen, Jamilu Kerawa ya tabbatar da afkuwar wannan farmaki, inda ya kara da cewa, barayin sun gudanar da ayyukansu ba tare da fuskantar wani kalu-bale ba. sun yi awon gaba da mutum sha biyu, mata goma maa biyu bayan sun kasha mutum guda. Sun kuma raunata wani mutum wanda aka garzaya das hi zuwa Asibiti a Zariya.
Muna bukata taimako a Kerawa, Allah ne kadai ke tsare da mu.
Ya bukaci gwamnatin Jihar Kaduna da ta tura jamian tsaro a yankin domin kauce ma karuwar farmaki a yankin.
Sai har ya zuwa hada wannan rahoto, ba a ji wani Karin haske ba daga gwamnatin jihar, haka kumka, ba a sami jin tab akin mai Magana da yawun rundunar yan sandan jihar ba.