
Daga Ahmed Kabir S/kuka a Katsina
An ta yada wasu bayanai gami da hotona akan gina wasu masallatai guda biyu, daya a garin Rimi, daya a garin Abukur dukkan su a qaramar hukumar Rimin dake Jahar Katsina wadanda wata qungiyar larabawa daga qasar Saudiya mai suna “Rabi’atul Alamil Islam ta gina.
Labaran da suka ja hankalin jama’a musamman akan wani zargi da aka azawa kauran Katsina Hakimin na Rimi Alhaji Nuhu Abdulqadir akan cewa ya kwacewa ‘Yan dadika bayan sune suka sayi fili da kuma gina wannan masallaci dake bisa kan hanyar zuwa kasuwar ta Rimi.
Abcnews ta bi sawun wannan labari inda domin samo sahihan bayanai akan wannan batu.
A binciken da wakilim Abcnews na Jahar Katsina yayi, ya samo bayanan dake cewa, shi dai wannan masallatai wadanda waccan kungiya ta gina an samo su ta hanyar wani dan siyasa kuma daya daga cikin masu rike da mukami a gwamnatin Jahar, wato, Injiniya Surajo Yazid wanda ya samu damar kawo wannan aiki ta hanyar wani abokin shi wanda sune wannan kungiya ke baiwa aikin.
A bayanan da muka samu daga bangarorin biyu, wato, kungiyar Izala da kuma ta darikar sun tabbatar da cewa, shi Injiniya Surajo shi ne wanda ya sayi filin da aka gina wannan masallaci na garin Rimi domin a tsarin kungiyar, fili ake basu su kuma su gina masallacin bisa wasu sharuddan da sukan gindaya.
Daga cikin sharuddan akwai hanawa mabiya Shi’a da kuma hana yin Waziha ko wani abu makamancin hakan.
A takaice, duk da basu cewa ga irin mabiyan da za’a ba masallacin idan sun gina, bayanai sun nuna cewa, kashi 80 cikin xari irin waxannan masallatai sukan shiga hannun qungiyar Izala ne.
Bayan kammala gina wadannan masallatai dukkan kungiyoyin biyu sun ta so da nufin samun wannan masallaci, yunkurin da ya kai su har zuwa ga shi Injiniya Surajo wanda wasu suka yi zargin cewa, yace, ‘Yan darika ya bada, ganin cewa an samu rashin jituwa tun daga lokacin da shi Kauran ya mika babban masallacin juma’ar dake fadar shi ga wanda su ‘Yan dariqar suka ce dan Izala ne aka ba bayan can baya sune ke jan salla a masallacin.
Wannan takaddamar mallakar wannan masallaci tayi zafi sosai wadda ta kai har sai da Kwamishinan ‘Yansandan Jahar CP Sanusi Buba ya je garin na Rimi inda aka tara dukkan bangarorin domin bin hanya mafi saukin warware wannan matsala.
Abcnews ta samu labarin cewa, daga cikin hanyoyin da aka bi har da batun cewa, shi wancan masallacin na garin Abukur a baiwa su ‘Yan darikar, tayin da suka ki amincewa da shi bisa nunin su na cewa, ai an hana masu wancan masallaci, wanda binciken Abcnews ya samu bayanin cewa, waccan kwacewar masallaci da shi Kauran yayi, ya amshe limancin ne daga shi limamin bisa dalilin cewa, ya koma tafarkin Shi’anci abin da su kuma basu yarda da hakan ba.
Kamar yadda binciken ya nuna, bayan yunkiri da kuma neman hanyoyin shawo kan waccan matsala ko rashin jituwa akan wannan masallaci wanda yake ba wanda za’a yi sallar Juma’a acikin shi ba ne, ance, da abin yayi zafi sosai tare kuma da ci gaba da tuntubar shi wanda ta hannun shi aka samu wannan aiki, karshe ya mayar da batun hannun shi Kauran domin kamar yadda muka ji, ance yace, Kauran ne zai bayar da masallacin ga inda ya dace, bayan su mabiya Izalar sunce sun janye daga bukatar mallakar masallacin.
Duk da kokarin da Abcnews tayi domin jin ta bakin shi Kauran abin ya ci tura, amma majiya mai qarfi ta tabbatarwa Abcnews cewa, Kaura ya bayar da limamin da zai jagoranci wannan masallaci daga bangaren su ‘Yan dariqar, abin da har ila yau bai yiwa wasu daga cikin mabiyan dadi ba, musamman masu aiwatar da Wazihar.
Sabon Limamin duk da yana daga bangaren dariqar ance, baya da wannan tsatsauran ra’ayin, hakan ne ya karawa sashen Izalar amincewa da wannan hukunci da shi Kauran ya dauka kamar yadda daya daga cikin wadanda suka wakilci kungiyar(an sakaya suna) ya shaida .
An kuma bayar da masallacin dai bisa sharuddan wadanda suka gina shi. To sai kuma su masu tsaurin ra’ayin musamman masu yin Wazihar, ance kwatsam, sai suka zo da zummar cewa lallai sai sun yi Wazihar, wasu ma sunce sai ma da suka yi, wanda wannan mataki ya nemi sake tayar da wata husumar musamman a tsakanin su, domin wasu na cewa, sai anyi wazifar yayin da wasu ke cewa, tunda bashi kadai ne gare su ba a tafi wani masallacin ayi.
Duk wani yunkuri na ganin shi Injiniya Surajo wanda ya hada da aika mashi da wasikar kar ta kwana na neman ji daga bakin shi tare da kiran waya, abubuwan da bamu samu ko daya daga wajen shi ba har zuwa rubuta wannan rahoto.
Makaryata kawai Allah zai tambaye ku, zaku maimaita wannan gobe kiyama